Belarus ta ce ana shirin kai wa Rasha hari

Belarus ta ce ana shirin kai wa Rasha hari
Yayin da dangantaka ke tsami tsakanin Rasha da kasashen yammacin duniya, gwamnatin Belarus ta ce akwai wani shiri da ta gano na kai wa Rasha hari daga yamma.

Shugaba Alexander Lukashenko na kasar Belarus, ya yi ikrarin cewa kasashen yammacin duniya na shirin kai wa Rasha hari ta kasar Ukraine da ma ta ita kanta Belarus.

Shugaba Lukashenko wanda ke jawabi lokacin bikin yaye manya da kananan hafoshin sojan kasar da aka yi a yau, ya ce tuni suka tattauna da Shugaba Putin na Rasha a kan wannan batu.

Belarus wacce babbar kawa ce ga Rasha, na dauke da sansanonin da dakarun Rasha ke cikin su kuma daga nan suna kai wa makwabciyarta Ukraine munanan hare-hare.

Kasashen yammacin duniyar dai ba su fito fili, sun bayyana shirinsu na kai wa Rasha hari ba duk da zafin yakin da gwamnatin Shugaba Putin ta kaddamar kan Ukraine da suke ji.


News Source:   DW (dw.com)