Batun kafa gwamnati a Austriya ya rushe

An fara tattaunawa domin kafa gwamnatin kawance mai jam'iyyu uku a kasar Austriya ne cikin watan Oktobar shekarar da ta gabata ta 2024, lokacin da shugaban kasar ya umarci shugaban gwamnati Karl Nehammer ya tattauna batun kafa gwamnati ta gaba. An gaza cimma matsaya tsakanin manyan jam'iyyun uku, kasancewar kowacce cikinsu ta yi watsi da tattaunawa da jam'iyyar Freedom Party mai matsanancin ra'ayi da kuma ke kan gaba a zaben na watan Satumbar bara. Shugaban gwamnatin na Austriya ya nemi kafa gwamnatin da jam'iyyun da suke da matsakaicin ra'ayi, amma hakan ya ci tura. Kasar ta Austriya dai, na cikin kasashen Turai da masu matsanacin ra'ayi ke kara samun kwarjini.


News Source:   DW (dw.com)