Barnar ababen fashewa a Jamus

Abin da ya fashen dai  ya yi matukar kara tada hankulan matsauna birnin da ke yammacin Jamus, wanda aka yi ta samun irin wadannan kananan fashewar abubuwa a baya-bayan nan. A cewar 'yan sandan birnin, mazauna kusa da kantin sayar da shayin da sayyin safiyar yau suka bada rahoton fashewar wani abun da tada hankalin mazauna a anguwar da lamarin ya faru. Daga fashewar abun sai gobara ta kama a kantin wanda ke karkashin gidajen kwana. A cewar kakakin 'yan sandan birnin, kawo yanzu basu kai ga tabbatar da abin da ya fashen ko kuma musabbabinsa, suna dai binciken ko yana daga cikin jerin irin fashe-fashen abubuwa da birnin na Kolon ya yi ta samu a 'yan kwanakin nan. Wani mazaunin kusa da kantin sayar da shayin, yace mai kantin kwanan nan ya bude, kuma yanzu ma dai baya gari ya tafi hutu. Mutum biyu sun dan jikkata daga hayakin gobarar, kuma akalla mazaunan gidajen wajen mutune 20 a ka sakewa wajen zama  sakamakon fashewar. A makon da ya gabata ma an samu fahsewar abubuwa har sau biyu a birnin na Kolon dake zama na hudu a jerin manyan biranen Jamus.


News Source:   DW (dw.com)