Majalisar Dinkin Duniya ta ce, ta gano wani sabon shirin Koriya ta Arewa na soma gwajin makaman nukiliya. A binciken sirri da ta ce ta gudanar, an gano yadda Pyongyang ta soma wasu aikace-aikacen kera makaman masu hadari a wani kebabben wuri da ke a yankin arewacin kasar. Rahoton ya kuma yi gargadin karuwar samar da sinadarin Uranium da aka inganta a wasu wurare a Koriya ta Arewa.
Kasashen duniya da dama, sun sha danganta gwajin makaman nukiliyan da Koriya ta Arewa ke yi a matsayin babbar barazana. Majalisar Dinkin Duniya ta yi kakkausar suka da kuma barazanar daukar mataki. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Chaina ta soma harba wasu makamai masu linzami a cikin tekun da ke kusa da makwabciyarta Taiwan dama yi wa tsibirin kawanya, bayan da ta fusata da ziyarar Shugabar Majalisar Wakilan kasar Amirka Nancy Pelosi a Taiwan din.