Barazana Turkiyya ga Finland da Sweden

Barazana Turkiyya ga Finland da Sweden
Turkiyya na kalubalantar kasashen Finland da Sweden a kan bukatarsu ta shiga kungiar tsaro ta NATO.

Turkiyya na zargin kasashen da kin amincewa da bukatar da ta gabatar musu na mika mutanen da ta zarga da kasancewa 'yan kungiyoyin ta'adda. Hukumomin Ankara sun yi  barazanar cewar za su toshe hanyar fadada shirin shigar da kasashen biyu, na arewacin Turai a cikin runduna tsaron ta NATO. Turkiyyar ta ce babu wasu daga cikin buƙatun tusa keyar mutane 33  da ta aika da ya sami ammsa mai kyau daga Stockholm ko Helsinki a cikin shekaru biyar da suka gabata. Gwamnatin ta Turkiyya na nema mutanen  ruwa jallo saboda kasancewarsu 'yan kungiyar PKK da ke da alaka da Fethullah Gülen wanda gwamnatin ke zargi da kitsa yunkurin juyin mulkin a ya ci tura a shekar ta 2016.

 


News Source:   DW (dw.com)