Bankin duniya zai kalubalanci karancin abinci

Bankin duniya zai kalubalanci karancin abinci
Bankin duniya ya bayyana samar da karin dala biliyan 12 domin amfani da su wajen rage radadin mummunar barazanar nan ta karancin abinci da duniya ke fuskanta.

An dai danganta karancin abincin a duniya ne, da matsaloli masu nasaba da sauyin yanayi da ma afka wa kasar Ukraine da yaki da Rasha ta yi.

Matakin na wannan lokacin, na nuna cewa bankin zai yi amfani ne da dala biliyan 30 jimilla a cikin watanni 15 nan gaba.

Sanarwar bankin na zuwa ne sa'o'i kafin wani taro da MDD ta shirya yi a kan barazanar karancin abincin a duniya.

Yankunan da matsalar ta fi shafa dai, su ne kasashen nahiyar Afirka da yankin Gabas ta Tsakiya da gabashin Turai, sai kuma tsakiya da ma wasu kasashen kudancin nahiyar Asiya.


News Source:   DW (dw.com)