Bankin duniya ya ba Afirka tallafin dala biliyan 3

Bankin duniya ya ba Afirka tallafin dala biliyan 3
Kasashen da ke fama da matsalar karancin abinci a kudanci da gabashin nahiyar Afirka, za su ci gajiyar tallafin kudi har dala biliyan 2 da 300 daga bankin duniya don yaki da matsalar fari da rashin tsaro.

Shirin bankin duniyar ya zai mayar da hankali ne kan kimanin mutane fiye da miliyan 66 a wadannan yankunan Afirka da aka yi ahsashen za su fuskanci matsalar abinci a watan Yuli na shekarar 2022.

Za kuma afara aiwatar da shirin ne daga kasar Habasha, inda kusan mutane miliyan 22 da 700 ke fama da karancin abinci  sanadiyyar matsalar fari, sai kuma kasar Madagaska inda mutane miliyan 7 da 800 suma ke cikin bukatar agajin abinci na gaggawa sakamakon rashin ruwa da ya haifar da fari a kudancin kasar.


News Source:   DW (dw.com)