Hukumar Lafiya ta Duniya WHO tare da likitoci a arewa maso yammacin Kongo sun sanar da barkewar wata cuta da ba kai ga gano ko wacce ce ba.
Sanarwar ta ce ya zuwa yanzu cutar ta kashe sama da mutum 50, kuma tazarar sa'o'i 48 ne kawai tsakanin alamomin bullarta da kuma mutuwa ga akasarin mutane.
Kashin farko na alluran rigakafin kyandar biri ya isa DRC
Darektan wani asibiti mai suna Bikoro Hospital Serge Ngalebato ya fada wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa lamarin cutar na da matukar sarkakiya da kuma damuwa.
Tun a ranar 21 ga watan Janairu ne cutar ta bulla kuma an samu rahotannin mutane 419 da suka kamu baya ga wasu 52 da suka rasu a sakamakon bakuwar cutar.
Ofishin Hukumar Lafiya ta Duniya na Afirka ya ce rahoton bullar cutar na farko shi ne na garin Boloko bayan wasu yara uku sun ci jemage kuma suka kamu da zazzafin zazzabi tare da mutuwa cikin sa'o'i 48.
Kabila ya caccaki Tshisekedi kan yakin Kongo
An jima ana nuna damuwa kan yadda cututtuka da ake samu daga cin naman dabbobi ke da wuyar sha'ani idan suka barke musamman a wuraren da mutane suka mayar da namun dawa tamkar tuwo.
Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo na da tarihin barkewar cututtuka kuma ko a shekarar da ta gabata ma wata cutar da ba kai ga gano sunanta ba ta barke tare da halaka mutane.