Bajamushiyar 'yar Iran Nahid Taghavi wadda mahukunkan Tehran suka kama a watan Oktoban 2020 ta shaki iskar 'yanci, kuma tun tuni ta isa Jamus a ranar Lahadi kamar yadda 'yarta da kuma kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International suka sanar.
A cikin wata sanarwa Amnesty International ta ce an saki Nahid Taghavi mai shekaru 70 a duniya bayan ta share kwanaki 1,500 a tsare ba bisa ka'ida ba, kuma ta isa cikin iyalinta lami lafiya.
Da take tsokaci kan batun a shafinta na X, ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ta bayyana dowowar matar cikin iyalinta a matsayin babban abin farin ciki bayan shafe shekaru hudu a gidan yari cikin yanayin ukuba.
Sakin Nahid Taghavi na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin tattaunawa kan shirin Iran na nukiliya a kasar Switzerland, mako guda gabanin rantsar da sabon shugaban Amurka Donald Trump.