Baerbock na ziyara a Mali

Baerbock na ziyara a Mali
Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock na ziyarar aiki a kasar Mali da ke yammacin Afirka.

Ziyarar na zuwa ne jim kadan bayan da kungiyar tarayyar Turai ta ce zata dakatar da bayar da horo ga dakarunta da ke kasar.

Berlin da ke zama fadar gwamnatin Jamus na duba yiwuwar kara tsawaita wa'adin zaman dakarunta na Bundeswehr a kasar yayin da ake nuna fargaba kan ayyaukan sojojin haya na kamfanin Wagner da Malin ta dauko daga Rasha.

Jamus dai na da dakaru fiye da dubu daya da ke cikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta MINUSMA.

A halin yanzu dai Baerbock ta gana da dakarun Jamus da ke sansanin Castor a Gao da ke arewacin Malin, kuma ake sa ran gaba ta gana da gwamnatin mulkin sojin kasar da ma kungiyoyin fararen hula.
 


News Source:   DW (dw.com)