
Allah ya yi wa babban sakataren kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta duniya OPEC Dr Mohammad Sunusi Barkindo rasuwa a daren jiya Talata.
A sanarwar da shugaban kamfanin man Najeriya NNPC Male Kyari ya fidda da wannan safiyar a shafinsa na Twitter, ya bayyana rasuwar Barkindo a matsayin babban rashi ga iyalansa da ma'aikatan kamfanin NNPC da ma kungiyar OPEC.
Barkindo ya rasu yana da shekaru 63 a duniya, kafin rasuwar sa, marigayin na gab da sauka daga mukaminsa na sakataren OPEC bayan kwashe sama da shekaru shida.
Ana sa ran a gaba a yau ne za a fidda bayanai a game da jana'izarsa.
News Source: DW (dw.com)