Ba tabbas kan zargin laifukan yaki kan Rasha - MDD

Ba tabbas kan zargin laifukan yaki kan Rasha - MDD
Kwamitin Majalisar Dinkin Duniya a Ukraine, ya tabbatar da samun zarge-zarge da dama na cin zarafin da sojojin Rasha ke yi, amma ya ce ya yi wuri a bayyana ko sun kunshi laifukan yaki.

Shugaban hukumar Erik Mose ya shaidawa taron manema labarai a Kyiv cewa, "A Bucha da Irpin, hukumar ta samu bayanai game da kashe-kashen jama'a ba bisa ka'ida ba, da barna da sace-sacen dukiya, da kuma hare-haren da ake kai wa fararen hula ciki har da makarantu."

A yankunan Kharkiv da Sumy, hukumar ta lura da "lalacewar manyan biranen kasar, wanda aka yi imanin ya samo asali ne sakamakon tashin bama-bamai da jiragen sama, da harsasai ko kuma harin makami mau linzami kan fararen hula," in ji shi.

Sai dai Moses ya ce Majalisar Dinkin Duniya ba ta da wani matsayi a wannan mataki na samar da cikakken bayanin abubuwan da suka faru a kusa da Kyiv a watan Maris.

Ya ce shaidun da hukumar ta tattara za su iya "idan an tabbatar da su daga baya" za su goyi bayan zarge-zargen take hakkin dan Adam, "ciki har da laifuffukan yaki da cin zarafin bil'adama".

Kalaman nasa sun zo ne a daidai lokacin da kwamitin bincike na kasa da kasa mai zaman kansa kan Ukraine, wanda kwamitin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya ya kafa a watan Maris, ke shirin kammala aikinsa na farko, wanda ya fara a ranar 7 ga watan Yuni kuma zai kare a ranar Alhamis.


News Source:   DW (dw.com)