Ba bukatar gargadi kan shirin nukiliyar Iran

Kamfanin dillancin labaran Iran IRNA ne ya ruwaito hakan, inda ya ce jakadan Tehran din a Majalisar Dinkin Duniya Amir Saeid Iravani ya nunar da cewa ksashen Faransa da Jamus da Ingila da ake kira da E3 da kuma Amurka na kokarin sanya siyasa cikin lamarin da nufin hana samar da mafita ta diplomasiyya. A cewar Irvani Tehran na bai wa Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya (IAEA) hadin kai saboda haka babu wani dalili da za a gabatar da wannan gargadi, sai dai kawai domin kasashen na E3 da Amurka da Rasha da Chaina na son yin amfani da wannan damar su kara kakaba takunkumi ga Iran. Kasashen na E3 da kuma sauran masu ruwa da tsaki kan yarjejeniyar nukiliyar Iran din ta 2025  ne dai, suka yi kira ga Tehran kan ta sake waiwayar shirinta na nukiliya a ranar tara ga wannan wata na Disamba da muke ciki a wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fitar.


News Source:   DW (dw.com)