Austria: Jam'iyyar FPÖ za ta kafa gwamnati

Bukatar Van der Bellen ya jagoranci kafa gwamnatin ta zo bayan da shugaban gwamnatin Karl Nehammer ya mika takardar yin murabus a ranar Asabar sakamakon rushewar tattaunawa ta hadakar gwamnatin wadda ba ta kunshi jam'iyyar FPO ba.

Kickl ya sami nasara a zaben majalisun dokokin Austria da ya gudana a watan Satumba da kashi 28.8 cikin dari na kuri'iun da aka kada inda ya kada Jam'iyyar yan mazan jiya ta shugaban gwamnati mai barin gado da ta zoi ta biyu.

Sai dai kuma Van der Bellen na da gagarumin kalubale na kafa sabuwar gwamnati kasancewar babu wata Jam'iyya da ke son yin aiki Kickl.

 


News Source:   DW (dw.com)