Taron zai tattauna batun karancin abinci da ke yin barazana ga wasu kasashe Afirka da ke bukatar agajin jin kai da batun ta'addanci da kuma juye-juyen mulki a Afirka.
An shirya shugabannin kasashen Afirka kusan 20 za su halarci taron. Kimanin mutane miliyan 113 ke bukatar agajin jin kai a Afirka, wadanda miliyan 48 daga cikinsu 'yan gudun hijira ne, masu neman mafaka. A cikin wata sanarwa da kungiyar ta AU ta fitar ta ce akwai bukatar agajin gaggawa a kasashen Afirka 15 da suka fi shafuwa.
News Source: DW (dw.com)