AU za ta tattauna batun abinci a Malabo

AU za ta tattauna batun abinci a Malabo
Taron zai tattauna batun karancin abinci da ke yin barazana ga wasu kasashen Afirka da ke bukatar agajin jin kai da batun ta'addanci da kuma juye-juyen mulki a Afirka.

An shirya shugabannin kasashen Afirka kusan 20 za su halarci taron. Kimanin mutane miliyan 113 ke bukatar agajin jin kai a Afirka, wadanda miliyan 48 daga cikinsu 'yan gudun hijira ne, masu neman mafaka.

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta AU ta fitar, ta ce akwai bukatar agajin gaggawa a kasashen Afirka 15 da suka fi shafuwa.

 


News Source:   DW (dw.com)