AU ta nuna damuwarta kan matakin Amurka na ficewa daga WHO

Shugaban Hukumar zartaswa ta Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat ya nuna damuwarsa kan matakin Trump na janye wa daga WHO, kasancewar Amurka ce ke ba da kaso mafi tsoka na tallafin da hukumar take samu daga kasashen duniya, wanda galibin tallafin na shafar nahiyar Afirka kai tsaye musamman rigakafin kyandar birrai da annobar Marburg da sauran al'amura na kiwon lafiya da ke bukatar daukin gaggawa.

Karin bayani: An samu bullar sabon nau'in COVID-19

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da annobar masassarar tsuntsaye ta bulla a Amurka, wanda hakan ya jefa rayuwar mutane da dama cikin mawuyacin hali. Kazalika matakin na zuwa a daidai gabar da mambobin kasashen da ke yarjejeniyar WHO ke shirin tattaunawa don tunkarar barazanar annobar da za a iya fuskanta a nan gaba tun bayan bullar annobar Covid 19 a 2021, inda za a gudanar da taron ba tare da wakilcin Amurka ba.

 


News Source:   DW (dw.com)