AU ta fusata da mutuwar 'yan ci ranin Afirka

AU ta fusata da mutuwar 'yan ci ranin Afirka
A cikin sanarwar da AU ta fitar ta yi kira da aka kaddamar da bincike, sannan ta tunasar da kasashe da su rika mutunta 'yan ci rani kamar yadda dokoki suka yi tanadin hana amfani da karfi a kan 'yan ci rani.

Shugaban hukumar gudanarwa ta Kungiyar Tarayyar Afirka, AU, Moussa Faki Mahamat ya nuna bacin ransa a game da rahotan mutuwar 'yan ci ranin Afirka 23 da ake zargin an gallaza wa azaba kafin mutuwarsu a kokarin da suka yi na shiga kasar Spain daga Moroko.
A ranar Jumma'a ce dai aka yi artabu a tsakanin 'yan ci rani wurin 2,000 da suka yi yunkurin tsallakawa Spain daga iyakar Moroko da kuma jami'an tsaro, lamarin da ya haifar da tashin hankalin da ya yi ajalin mutum 23. 
 


News Source:   DW (dw.com)