Aski ya zo gaban goshi a zaben shugaban Amurka

'Yar takarar shugabancin kasar a jam'iyyar Democrats Kamala Harris za ta karkare yakin neman zabenta a Pennsylvania, dake da yawan kuri'un da ke da tasiri a yawan wakilai na musamman da aka fi sani da Electoral College, wadanda su ke tabbatar da nasarar shugaban kasa bayan an kammala kada kuri'a a hukumance.

Karin bayani: Harris da Trump na kace-nace a gangamin yakin neman zaben Amurka

A gefe guda, 'dan takara a jam'iyyar Republican Donald Trump na ta kai komo a jihohin uku da suka hadar da North Carolina tare kuma da yada zango har sau biyu a Pennsylvania.

Karin bayani: Kamala Harris na samun goyon bayan 'yan Democrat 

Yakin Gaza da batun bakin haure da dokar zubar da ciki da yakin Ukraine da Rasha da harkokin sauyin yanayi har ma da batun inshorar lafiya na daga cikin muhimman batutuwan da 'yan takarar suka tafka muhawara a kai wajen zawarcin kuri'un Amurkawa.

 


News Source:   DW (dw.com)