Arangama a masallacin Al Aqsa

Arangama a masallacin Al Aqsa
Falasdinawa da 'yan sandan Israila sun yi arangama a masallacin Al-Aqsa a yankin birnin Kudus yayin da dubban jama'a suka hallara domin sallar Juma'a, arangamar da ke zama ta farko tun bayan fara azumin watan Ramadan.

Jami'an kiwon lafiya sun ce Falasdinawa fiye da 150 suka sami raunuka yayin mummunar arangamar.

Wurin idabar wanda ke zama wuri mai tsarki ga Musulmi da Yahudawa ya kasance inda ake yawan samun tashin hankali tsakanin Israila da Falasdinawa. 'Yan sandan Israila sun ce sun kama mutane kimanin 400

Jakadan musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Gabas Ta Tsakiya Tor Wennesland ya bukaci hukumomi a bangarorin biyu su gaggauta kwantar da hankula domin hana cigaba da tada hankali.

Arangamar da aka yi a wannan wuri a bara ta haifar da yakin kwana goma sha daya da 'yan Hamas a zirin Gaza. Wannan arangamar da na zuwa ne a lokaci mai muhimmanci ga mabiya addinan biyu.

Azumin bana ya zo a daidai lokacin da ake bikin Passover babbar ranar hutu ga Yahudawa da ya fara a wannan Juma'ar kuma mako mai tsarki ga Kiristoci wanda ke karewa da bikin Easter a ranar lahadi.

Dubun dubatan mabiya addinan za su hadu a tsohon birnin Kudus da ke dauke da wurare masu tsarki ga mabiya addinan uku.
 


News Source:   DW (dw.com)