Antony Blinken zai kai ziyara a Afirka

Antony Blinken zai kai ziyara a Afirka
Ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta ce jagoran diflomasiyyar Amirkar zai kai ziyara a cikin kasashen Afirka ta Kudu,da Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango da Ruwanda,a cikin watan Agusta da ke shirin kamawa.

Antony Blinken zai yi rangandi ne a wani yunkuri na dakile fafutikar da Rasha take yi na samun goyon baya a nahiyar Afrika, da kuma nuna muhimmanci hulda da Afrika. An shirya Jakadiyar Amirka a Majalisar Dinkin Duniya, Linda Thomas-Greenfield, za ta ziyarci kasashen Ghana da Uganda a wata mai zuwa, bayan da darektan hukumar ba da agaji ta Amirka Samantha Power ta kammala ziyarar da ta kai a Kenya. Yunkurin diflomasiyya na Amirka na zuwa ne a daidai lokacin da ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov ya fara rangadin a cikin wasu kasashen Afirkan,inda ya dora laifin hauhawar farashin kayan abinci a kan takunkumin da kasashen yamma suka kakabama kasarsa, furcin da Amirka ta yi watsi da shi.

     

 


News Source:   DW (dw.com)