Sakataren harkokin wajen Amirka, Antony Blinken ya isa birnin Tel Aviv na Isra'ila a ziyarar da yake yi a yankin Gabas ta tsakiya domin bayar da gudunmawar cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Zirin da ma sakin wadanda kungiyar Hamas ke ci gaba da tsare su.
Karin bayani: Blinken na matsa wa Isra'ila lamba don tsagaita wuta a Gaza
A ziyararsa a karo na tara a yankin, Blinken zai gana da manyan shugabannin Isra'ila da ma Firanministan kasar, Benjamin Netanyahu; kafin daga bisani ya isa kasar Masar inda za a ci gaba da tattaunawa da sauran masu shiga tsakani a rikicin.
Mista Blinken ya ce, watakila tattaunawar ta wannan lokacin ta kasance dama ta karshe ta cimma yarjejeniyar kawo karshen yakin. Ya kara da cewa, za su yi dukannin mai yiwuwa wajen ganin cewa yakin bai ta'azzara ba ko ma ya yadu zuwa wasu sassan.