Sakataran Majalisar Dinkin Duniyar ya isa a Ukraine daga birnin Moscow inda ya roki Vladimir Putin da ya tsagaita bude wuta. Guteres ya ce ya damu matuka da rahotannin da ake ta yi na yiwuwar aikata laifukan yaki, yana mai cewa suna bukatar bincike mai zaman kansa. Sannan zai tattauna da shugaban Ukraine ganin ta yadda za a ceto farar hula da suka makele a birnin Mariuopol.