Babban sakataren harkokin wajen Amirka Anthony Blinken zai tattauna da hukumomin kasashen Afrika ta Kudu da Ruwanda da kuma Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kongo ne kan muhimman batutuwa musamman ma mamayar da kasar Rasha ke yi wa Ukraine, duk da yake wasu bayanai na cewa Anthony Blinken zai tattauna batun zaman lafiya a gabashin Kongo. Burin wannan ziyarar in ji Anthony Blinken shi ne na rage karfin tasirin da Rasha take da shi a wasu kasashen nahiyar Afirka ta fannin diflomasiyya. Afirka ta Kudun da ke zama daya daga manyan kasashen Afirka masu tasowa, ta kasa daukar wani muhimmin mataki kan mamayar da Rasha ta ke yi wa Ukraine tun bayan da aka soma gwabza yaki.
Ministan harkokin wajen Amirka Anthony Blinken ya isa birnin Pretoriya na Afirka ta Kudu a cigaba da rangadin da ya soma gudanarwa cikin wasu kasashen nahiyar Afirka.