Kamfanin Lucapa mallakin kasar Ostireliya da ke aikin hakar ma'adanan ne ya sanar wa da hukumomin Angola a Larabar nan cewa ya hako lu'u-lu'un mai nauyin carat 170 da kuma aka yi wa lakabi da Lulo Rose.
Ana fatar lu'u-lu'un mai ruwan hoda zai kawo wa Angola makudan kudade, domin kafin yanzu, rahotanni sun ce babban lu'u-lu'u mai tsada a duniya shi ne mai nauyin carat 59.6 wanda aka sayar a shekarar 2017 a birnin Hong Kong a kan kudi Euro miliyan 70. To sai dai kuma akwai yiwuwar nauyin lu'u-lu'un na Angola ya ragu daga nauyinsa na carat 170 bayan an wanke shi.