A wannan Lahadin Faransawa za su kada kuri'unsu na zaben shugaban kasar a zaben da ke kasancewa zagaye na biyu a tsakanin Shugaba mai ci Emmanuel Macron mai sassaucin ra'ayi da abokiyar takararsa Marine Le Pen ta masu matsanancin ra'ayin rikau. Tun daga karfe shida agogon GMT ake bude rumfunan zaben.
Kowanne daga cikin 'yan takara biyu na fuskantar kalubale na dabam, a bangaren Shugaba Macron ana ganin gazawarsa kan kasa cika alkawarin da ya daukar ma 'yan kasa bayan kama mulki a shekarar 2017 na kawo sauyi , maimakon hakan Faransawa na fama da tsadar rayuwa, a nata bangaren kalubalen Marine Le Pen ya karkata kan ra'ayinta na adawa da kwararar baki a Faransa da kuma batun neman hana sanya hijabi