Ana zaben shugaban kasa a Faransa

Ana zaben shugaban kasa a Faransa
A wannan Lahadin Faransawa ke kada kuri'ar bambance tsakanin aya da tsakuwa a zaben shugaban kasa da Macron mai sassaucin ra'ayi ke fafatawa da Le Pen ta masu ra'ayin rikau.

A wannan Lahadin Faransawa ke kada kuri'unsu na zaben shugaban kasar a zaben da ke kasancewa zagaye na biyu a tsakanin Shugaba mai ci Emmanuel Macron mai sassaucin ra'ayi da abokiyar takararsa Marine Le Pen ta masu matsanancin ra'ayin rikau. Tun daga karfe shida agogon GMT aka bude rumfunan zaben.

Kowanne daga cikin 'yan takarar biyu na fuskantar kalubale na daban, a bangaren Shugaba Macron ana ganin gazawarsa kan kasa cika alkawarin da ya daukar ma 'yan kasa bayan kama mulki a shekarar 2017 na kawo sauyi, maimakon hakan Faransawa na fama da tsadar rayuwa, a nata bangaren kalubalen Marine Le Pen ya karkata kan ra'ayinta na adawa da kwararar baki a Faransa da kuma batun neman hana sanya hijabi


News Source:   DW (dw.com)