Ana zaben sabon shugaban jam'iyyar mai mulkin Kanada

Jam'iyyar Liberal mai mulkin kasar Kanada ta ce ranar 9 ga watan Maris za ta bayyana sunan wanda zai karbi ragamar shugabancin jam'iyya da maye gurbin Firaminista Justin Trudeau wanda ya yi murabus. Trudeau zai ci gaba da rike mukamunsa na firaminista zuwa lokacin da jam'iyyar za ta yi sabon shugaba.

Karin Bayani: Mataimakiyar firaminista kana ministar kudin Kanada ta ajiye aiki

Manyan 'yan takara biyu a zaben neman shugabancin jam'iyyar mai mulkin Kanada su ne Mark Carney tsohon gwamnan babban bankin kasar da Chrystia Freeland tsohuwar ministar kudi, wadda murabus da ta yi a watan jiya ya kara kassara gwamnatin Firaminista Trudeau tare da janyo ya yi murabus.

Duk wanda ya samu nasarar zai karbi ragamar jam'iyyar Liberal da kuma mukamun firaminista har zuwa lokaci zaben kasa baki daya, inda masu kada kuri'a za su tantance makomar kasar na gaba.

 


News Source:   DW (dw.com)