Ana zaben raba gardama a Tunisiya

Ana zaben raba gardama a Tunisiya
A shekarar da ta gabata ne Shugaba Kais Saïed da aka zaba a shekarar 2019 a Tunisiya, ya rusa gwamnati da ma neman kara wa kansa karfin iko, abin da wasu ke cewa kama-karya ne.

Akalla mutum miliyan takwas ne za su kada kuri'a a zaben raba gardama da za a yi a yau Litinin domin sake fasalin kundin tsarin mulki a Tunisiya.

Zaben da Shugaba Kais Saïed ya tsara, na da manufar kara wa shugaban kasar karfin iko.

Hakan zai ba shi damar zartar da manyan matakai da ma iya nada jagororin gwamnati da ministoci.

Sai dai damar za ta rage wa majalisa karfi a Tunisiya, abin da tuni bangaren adawa ke kiran da a kaurace wa zaben.

A bara ne dai Shugaba Kais Saïed da aka zaba a shekarar 2019, ya rusa gwamnatin da ma majlisar dokokin kasar ya kuma bayar da hujjar kafa dokar ta baci.

Masu sukar lamirin gwamnati a Tunisiyar dai na cewa an koma mulkin kama-karya a kasar.


News Source:   DW (dw.com)