An bude rumfunan zabe a sassa daban-daban na kasar Australia, inda 'yan kasar za su zabi 'yan majalisar kasa.
Ana dai sa ran samun sakamakon da zai iya zama kusan kan-kan-kan, kuma ta yiwu jam'iyyar adawa ta Labor ta ba da mamaki kamar yadda kuri'ar jin ra'ayi ya nunar.
Jagoran adawar kasar ta Australia Anthony Albanese ya yi kiran da a juya wa Firaminista Scott Morrison baya, yana mai bayyana shi da mai manufofi na raba kan kasa.
Sama da mutum miliyan 17 za su kada kuria'a, inda za su zabi 'yan majalisar wakilai 151 da kuma 'yan majalisar dattawa 78.
Tuni ma dai fiye da rabin wadanda suka cancanci zabe suka riga suka kada kuri'arsu kafin wannan Asabar.