
Al'ummar kasar Denmark na kada kuri'a a zaben raba gardama kan shigarta cikin manufofin tsaro na tarayyar Turai, hakan kuwa ya biyo bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.
A tsawon shekaru 30 Denmak ta kasance a gefe da Turai ba tare da shiga cikin harkokin kungiyar ba Denmak memba a kungiyar ta tarrayar Turai tun a shekara ta 1972, it ace kasa ta farko da ta janye ta hanyar ƙin amincewa da yarjejeniyar Maastrich a shekara ta 1992. Sau biyu kasar tana shirya yin kuri'ar raba gardama kan shiga kungiyar ta EU a shekara ta 2000 da kuma 2015 amma jama'ar kasar suka yi watsi da bukatar.
News Source: DW (dw.com)