'Yan majalisar dokokin kasar Sri Lanka sun amince da batun zaben sabon shugaban kasa a makon gobe, sai dai sun tafka turanci a kan wadanda za a zaben domin jagorantar gwamnatin.
Babban dai batun da ya fi daukar hankali a zamansu na yau Talata, shi ne mutanen da za su iya tsamo kasar daga tarnaki na tattalin arziki da da ma tabarbarewar lamuran siyasa da ta shiga.
Sakamakon kokawa da tsananin karancin abinci da makamashi da ma magunguna da 'yan kasar suke yi, wasu fusattun 'yan Sri Lankan suka afka wa gidan Shugaba Gotabaya Rajapaksa da ma na Firaministan kasar a karhsen mako.
Karfi da ma tsananin boren da jami'an suka gani, sun sanya su amincewa da ajiye aiki daga bisani.