Ana shirin tsige shugaban Koriya ta Kudu

Kiraye-kirayen neman tsige shugaban kasar Koriya ta Kudu daga kan kujerarsa na ci gaba da karuwa a fadin kasar.

Dubban Koriyawa ne za su gudanar da tattaki a ranar Asabar a kokarin bai wa Majalisar Dokokin Kasar kwarin gwiwa domin kawar da shugaba Yoon Suk Yeol daga kan kujerarsa biyo bayan ayyana dokar soji ta sa'o'i shida a ranar Talata.

An kaddamar da gagarumin bincike kan shugaban Koriya ta Kudu

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban jam'iyya mai mulkin kasar ya goyi bayan dakatar da karfin ikon shugaba Yeol da kundin tsarin mulkin kasar ya bashi.

Har ila yau, sojin Koriya ta Kudu sun ce ba za su sake amincewa da umurnin aiwatar da dokar soji ba daga shugaban kasar ko kuma wani jami'i da zai bukace su da aiwatar da ita.

Koriya ta Kudu: 'yan siyasa da kungiyoyin kwadago sun bukaci shugaban kasa ya yi murabus

Shugaba Yoel ya shiga halin matsin lamba ne tun a ranar da ya ayyana dokar soji biyo bayan zargin barazanar kasa da bai bayyana inda take fitowa ba.

Majalisar Dokokin Koriyar ta na shirin kada kuri'ar tsige shi ko kuma a'a, a ranar Asabar, a yayin da 'yan adawa ke zawarcin ganin an raba shugaban da kujerarsa.


News Source:   DW (dw.com)