Tsigaggen shugaban kasar Koriya ta Kudu Yoon Suk Yeol na fuskantar shari'ar karshe kan tsigeshi da aka yi daga karagar mulki a ranar Talata.
Alkalai za su duba tabbatuwar tsigeshi da aka yi ko kuma a'a bayan kafa dokar soji a yayin da ya ke rike da madafun ikon kasar.
Koriya ta Kudu: Shugaba Yoon ya gurfana a gaban kotu
Matakin na mista Yoon ya jefa kasar da ke kan turbar dimokuradiyya cikin rudanin siyasa lamarin da ya sa majalisar dokoki ta tsige shi a watan Disambar 2024.
Tsohon shugaban kasar mai shekara 64 ya na garkame tun bayan damke shi da hukumomi suka yi a watan da ya gabata tare da fuskantar shari'a.
Shugaba Yoon ya ki bayar da kai bori ya hau— Masu bincike
Masu zan-zangar nuna goyon baya ga Yoon din sun hallara a wajen kotun tare da neman a wanke shi daga zarge-zargen da ake masa.
Zaman kotun na Talata shi ne na karshe kafun alkalai takwas su rufe kofa su kuma yanke hukunci kan makomarsa.