An bude runfunan zabe a kasar Amurka inda ake fafata zaben shugaban kasa mai zafi tsakanin Donald Trump na jam'iyyar Republikan da kuma Kamala Harris ta jam'iyyar Demokrat, inda duk wanda ya lashe zaben tsakanin mutanen biyu zai zama jagoran kasar ta Amurka na shekaru hudu masu zuwa, a kasar mafi karfin tattalin arziki tsakanin kasashen duniya.
Karin Bayani: Harris da Trump na kace-nace a gangamin yakin neman zaben Amurka
Ana kuma zaben 'yan majalisar dokoki domin sanin jam'iyyar da za ta karbe ragamar majalisun biyu na wakilai da dattawa. Kimanin mutane milyan 240 suka cancanci kada kuri'a a kasar ta Amurka.