Kungiyoyin kasa da kasa sun yi gargadi cewa rikicin da ke gudana a arewacin Sudan ta Kudu na iya haifar da mummunan tashin hankali a jaririyar kasar mai arzikin man fetur da kuma ke fama da talauci. Tun makonni biyun da suka gabata ne ake gwabza fada tsakanin sojojin Sudan ta Kudu da matasa da ke da dauke da makamai na SPLA/IO a gundumar Nasir ta jihar Upper Nile da ke kan iyaka da kasar Sudan.
Karin bayani: Salva Kiir zai yi tazarce a Sudan ta Kudu
MDD ta ce wadannan fadace-fadacen sun yi sanadiyar mutuwar fararen hula tare da jikkata wani sojan kiyaye zaman lafiya a kasar, da kuma uwa uba raba dubban mutane da muhallansu, a rikicin da ke hada Shugaba Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar. Hukumomin kasa da kasa da suka hada da Kungiyar Tarayyar Afirka ta IGAD sun bayyana damuwarsu dangane da tabarbarewar harkokin tsaro a jihar Upper Nile a makonnin baya-bayan nan, lamarin da ke ta'azzara rashin kwanciyar hankali a Sudan ta Kudu.