Zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a Saliyo ta kazance a wannan Laraba, inda ta yi ajalin 'yan sanda biyu. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce boren da aka yi shi a birnin Freetown, shelkwatar kasar, ya sanya katse kusan gaba daya hanyoyin sadarwa a kasar.
A wani jawabi na bidiyo da mataimakin shugaban kasar Mohamed Juldeh Jalloh ya fitar ya ce gwamnati ta sanya dokar hana shiga da fita a birnin Freetown domin bai wa jami'an tsaro damar shawo kan zanga-zangar da ta rikide ta koma tashin hankali.