Dubban masu zanga-zanga ne suka yi dafifi a Tunis babban birnin kasar Tunisiya, inda suke nuna turjiya ga zaben raba gardama da Shugaba Kais Saied ya tsara domin sauya kundin mulkin kasar.
Ana dai kallon yunkuri ne da shugaban na Tunisiya ke yi da nufin ci gaba da dorewa bisa mulkin kasar.
Haka ma Shugaba Saied din na neman sauyin ya bai wa fadar shugaban kasa karin karfin iko daidai lokacin da kasar ke cikin tarnaki na tattalin arziki.
Su ma dai kusan dukkanin jam'iyyun siyasar sun yi watsi da wannan yunkuri.
A ranar 25 ga watan gobe ne dai aka tsara gudanar da zaben na raba gardama a Tunisiyar.