An zargi Mali da kisan fararen hula

An zargi Mali da kisan fararen hula
Wani rahoton kungiyar kare hakin bil Adama ta Human Rights Watch ya zargi sojan Mali da kisan fararen hula akalla 300 bisa tuhumarsu da zama 'yan ta'adda a yankin Mura na kasar.

Kungiyar Human Rights Watch ta ce abubuwan da suka faru a Mura na zama mafi muni tun bayan barkewar rikici a kasar Mali a shekarar 2012, a yayin da ta tattara shedu 19 da suka hakikance kisan fararaen hula a yankin da sunan 'yan ta'adda.

A yanzu ya zama wajibi a cikin gaggawa hukumomin mulkin soja a Mali da su kaddamar da binicke na hadin gwiwa da kungiyoyin kasa da kasa kan zarge-zargen taka hakin bil'Adama, a cewar Corinne Dufka daraktar kungiyar Human Rights Watch a yankin Sahel.

Sai dai da ta ke mayar da martani a cikin wata sanarwar da ta fitar rundfunar tsaron kasar Mali ta yi fatali da zarge-zargen da ake yi mata, tana mai cewar wani yunkuri ne kawai na shafa mata kashin kaji.


News Source:   DW (dw.com)