An yi sakaci a katse aikin riga-kafi a Afirka

An yi sakaci a katse aikin riga-kafi a Afirka
Hukumar Lafiya ta Duniya ta baiyana damuwa kan yadda aka katse aikin riga-kafi na cututtuka a Afirka bayan da duniya ta mayar da hankali kan yakar cutar corona.

Annoba corona ta janyo katsewar aikin riga-kafi a kasashen Afirka, inda yanzu ake fuskantar kalubale daga cututtuka masu yaduwa. Reshen Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a Afirka, ya gano cewa, adadin wadanda cutar kyanda ta kama ya haura dubu goma sha bakwai a tsakanin watannin Janairu da Maris da suka gabata.

Hakazalika akwai kasashe kimanin ashirin da hudu da aka sake samun bullar cutar Polio ko Shan Inna, alkaluman da suka haura na bara, kuma hakan na a sakamakon yadda duniya ta kwashi kimanin shekaru biyu tana yakar annobar corona ba tare da ta bai wa wadannan cututtukan da ake iya amfani da allurar riga-kafi wajen dakilesu mahinmanci ba.

Hukumar ta WHO ta nemi a dauki matakin gaggawa a gudanar da riga-kafi wanda ya fi magani don ceto rayuka a Afirka kafin wanki hula ya kai dare.
 


News Source:   DW (dw.com)