Majalisar tsaro a Sudan ta bayar da shawarin janye dokar ta-baci da gwamnatin soji ka kafa a fadin kasar bayan kwace iko da ta yi a bara.
Bangaren tsaron na Sudan ya kuma nuna bukatar sakin duk wadanda gwamnati ke tsare da su bayan yamutsin da aka samu sakamakon sauyin gwamnati da aka samu a baran.
A ranar Lahadi ne dai shugaban gwamnatin Sudan din Janar Abdel Fatah al Burhan, ya jagoranci taron da ya maida hankali kan batutuwan tsaron kasar bayan kifar da gwamnatin dimukuradiyya a ranar 25 ga watan Oktoba.
A gefe guda kuma, a yau ne jakadan Majalisar Dinkin Duniya a kasar Volker Perthes ya nuna bacin ransa game da kisan wasu mutum biyu, a wani yunkurin tarwatsa masu zanga-zangar goyon bayan dimukuradiyya da jami'an tsaro suka yi.