An yi gwanjon rigar Diego Maradona

An yi gwanjon rigar Diego Maradona
An yi gwanjon rigar da fitaccen dan kwallon kafar nan dan kasar Argentina, marigayi Diego Maradona ya sanya a shekaru sama da 35 da suka gabata a kan miliyoyin daloli.

An sayar da rigar kwallo da marigayi Diego Armando Maradona, dan asalin kasar Argentina ya sanya a shekarun 1980 a kan kudi sama da dala miliyan tara.

Rigar ta Maradona mai lamba 10, ita ce ya sanya a wasan da ya ci Ingila da hannu a lokacin gasar kwallo ta duniya da aka yi a Mexico a shekara ta 1986. Ana minti shida da komawa bayan hutun rabin lokaci, Maradona ya jefa wa Ingila kwallon a raga.

Haka ma wasu mintuna hudu bayan nan, Diego Maradona ya sake cin wata kwallon da ta kasance daya daga cikin fitattu a tarihin gasar kwallon kafa ta duniya.

Dan wasan tsakiya na Ingila a wancan lokaci, Steve Hodge ya karbi rigar ta Maradona bayan tashi daga wasan, rigar da cikin watan jiya ya sanar da cewa zai yi gwanjon ta, bayan zaman shekaru 19 a gidan adana kayan tarihi na kasar.


News Source:   DW (dw.com)