An yanke wa 'yan adawa 16 hukunci kan yaudara a Yuganda

Wata kotun soji a Yuganda ta yanke hukunci kan mutum 16 'yan jam'iyyar adawa  ta NUP saboda samunsu da laifin yaudara, a cewar wani lauyan da ya kare mutanen. Kazalika, masu shari'ar sun same su da wasu karin mutane da suka yi layar zana da laifin mallakar abubuwa masu fashewa tun shekaru uku da suka wuce a yayin da aka doshi gudanar da zaben da ya gabata.

Lauyan wadanda aka yanke wa hukuncin Shamim Malende ya fadawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa akwai ayar tambaya kan yadda wasu daga cikinsu suka amince da laifin da suka musanta aikatawa a baya.

Karin bayani:MDD ta yi Allah-wadai da kisan 'yar gudun fanfalaki a Yuganda

Tsohon mawaki kuma fitaccen dan adawar kasar Robert Kyagulanyi da aka fi sani da Bobi Wine ya yi ikirarin cewa an tilasta wa mutanen amsa laifukan da ake tuhumarsu da aikatawa, domin neman afuwar da shugaban kasa ke yi wa fursunoni.

An dai haramta wa 'yanjarida halartar zaman kotun. Mutanen sun shafe shekaru hudu a gidan yari kuma za su bayyana agaban kotu a gobe Laraba domin jaddada hukuncin.

Karin bayani:Schoof: Za mu tura 'yan Afirka da ke neman mafaka a Yuganda

Kasar ta Yuganda na karkashin mulkin shugaba Yoweri Museveni tun a shekarar 1986 har ya zuwa yanzu.

 

 


News Source:   DW (dw.com)