An wanke Shell daga zargin cin hanci

An wanke Shell daga zargin cin hanci
Kotun birnin Milan na Italiya ta yi watsi da kara ta almundahana da aka zargi shugabannin kamfanonin hakar mai Eni da Shell da aikatawa a yarjejeniyar hako mai a Najeriya.

 A hukuncin da ya yanke, ofishin mai shigar da kara na Italiya ya ce  babu wata shaida da ke tabbatar da cewa Eni da Shell na cin hanci a harkar hako mai a Najeriya. Dama dai tun a watan Maris na 2021, wata kotu a Milan ta wanke kamfanin Eni na Italiya da kamfanin Shell da wadanda ake tuhuma 13 daga laifin da ake zarginsu da aikatawa.

Kungiyoyi masu zaman kansu guda uku ne suka shigar a shekarar 2013 a gaban kotu. Masu gabatar da kara sun fara zargin Eni da Shell da biya cin hancin na dala biliyan 1.1 don samun lasisin hako mai a Najeriya, da aka kiyasta yana dauke da ganga biliyan tara na danyen mai.

Duk da cewa an biya kudin ne ga gwamnatin Najeriya, masu gabatar da kara sun yi zargin cewa mafi yawansu na karewa ne a cikin aljihun 'yan siyasa da dillalan mai na Najeriya.

    


News Source:   DW (dw.com)