An cafke ministan tsaron kasar Bosnia a ranar Alhamis bisa tuhumar aikata laifin cin hanci da rashawa a yayin da ya jagoranci kamfanin ayyukan hanyoyi a kasar.
Nenad Nesic mai shekara 46 na daga cikin mutum shida da aka cika hannu da su a cewar masu sharia'a na kasar ta Bosnia da ke Kudu maso gabashin Turai.
Kotun MDD ta fara sauron karar kisan kiyashi a Bosnia
A wata sanarwa da aka karanta, an zargi mutanen da cin hanci da rashawa da yin sama da fadi da kudaden al'umma da amfani da mukamansu ta hanyar da bata dace ba da kuma karban na goro.
Nesic ya kasance ministan tsaron kasar tun a 2023 kuma shi ne shugaban jam'iyyar DPA da ke cikin kawancen jam'iyyu da ke mulki a kasar.
Croatia ta nemi afuwa dangane da yaƙin Bosnia
Sha'ar da ake yi wa mutanen za ta ci gaba kuma za a yanke musu hukunci daidai da laifin da suka aikata inji masu sha'ari'a.