'Yan takara 13 ne suka samun tikitin shiga zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa a ranar 7 ga watan Disamba a Ghana, domin zabar wanda zai gaje Nana Akufo-Addo, kamar yadda hukumar zaben kasar ta sanar. 'Yan takara biyu da aka fi kyauta musu zato dukkansu daga arewacin Ghana na cikin 'yan takara da aka tantance, wato mataimakin shugaban kasa Mahamudu Bawumia na jam'iyyar NPP mai mulki da kuma dan adawa John Mahama na jam'iyyar NDC. Shi dai Bawumia na NPP na neman ci gaba da rike mulki bayan Nana Akufo-Addo ya kare wa'adin mulki na biyu, yayin da Mahama ke kokarin komawa kan karagar mulki bayan faduwa zabe a shekara ta 2016.
Karin bayani: Ghana: Zaben fidda gwani na Jam'iyyar NPP
Sannan hukumar ta zabe ta amince da karin wasu 'yan takara tara daga jam'iyyu da kuma masu zaman kansu hudu, ciki har da Alan Kyerematen, tsohon ministan kasuwanci da kuma matashin dan kasuwa Nana Kwame Bediako, wanda ke samun goyon bayan matasan Ghana. Amma kuma hukumar ta yi watsi da takardun 'yan tkara 11 saboda ba su cika sharuda ba.
Karin bayani:Fargaba gabanin babban zabe a Ghana
Yakin neman zaben shugaban kasar Ghana ya fi mayar da hankali ne kan sauye-sauyen da za a yi gudanar domin fitar da kasar daga kangin tattalin arzikin da ya addabe ta, wanda shi ne mafi muni cikin shekaru da dama da suka gabata.