An sace wasu kayan tarihi na Holocaust a Jamus

Lamarin dai ya daure kan 'yan sandan yankin na Zeitz da suke ta tararrabin yadda aka sace duwatsun na alfarma da ke dauke da sunaye da shakarun haihuwa na wasu Yahudawa da sojojin Nazi suka halaka su. Galibin jihohin Jamus na da irin wadannan duwatsun da ake likasu a gefen tituna ko kuma a jikin gidajen mutanen da aka yiwa kisan kare dangi a lokacin yunkurin shafe Yahudawa daga doron kasa a zamanin mulkin 'yan Nazi.

Karin bayani: An karrama masu mu'amalar jinsi a taron ta'asar Holocaust

Magajiyar Garin birnin na Zeitz Kathrin Weber ta ce sace duwatsun na tarihi na da alaka da siyasa, a yankin da jam'iyyar AfD mai ra'ayin kyamar baki ke ci gaba da samun farin jini a Saxony.

karin bayani: Jamus: Jimami kan kama karyar 'yan Nazi

Sace kayan tarihin na zuwa a daidai lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da taron alhinin tunawa da Yahudawan da aka yi wa kisan kiyashi a yankin, da tuni mazauna yankin suka kaddamar da asusun tara kudin sake maye guraben duwatsun na tarihi.

 

 


News Source:   DW (dw.com)