An sace wani limamin Kirista a Najeriya

An sace wani limamin Kirista a Najeriya
A daidai lokacin da ake juyayin kisan gomman mabiya addinin Kirista a kudancin Najeriya, an tabbatar da sace wani malamin addinin na darikar Katholika a jihar Kogi.

Rahotannin da ke fitowa daga Najeriya, sun tabbatar da sace wani babban limamin addinin Kirista na darikar Katholika a garin Obangede da ke tsakiyar jihar Kogi.

Manyan jami'an Katholika da ke yankin, sun ce sun yi ta neman Father Christopher Itopa Onuto, wanda da ma shi ne zai jagoranci gabatar da addu'oi na musamman saboda ranar Pentecost, amma babu labarinsa.

Manyan na ikilisiya sun ce bayan bincike da suka gudanar ne suka iske kofofi da ma tagogin gidan Father Christopher a balle, an kuma tattara dukkanin kayayyakinsa.

An dai sace babban malamin na Katholika a jihar Kogi ne kafin mummunan harin nan da aka kai kan majami'ar Katholika da ke jihar Ondo inda aka yi asarar rayukan sama da mutum 50 a jiya Lahadi.


News Source:   DW (dw.com)