Shugaba Sergio Mattarella na Italiya ya rusa majalisar dokokin kasar jim kadan bayan karbar takardar marabus din firaminista Mario Draghi a wannan Alhamis.
Shugaba Mattarella ya ce ya dauki matakin rusa majalisar dokokin ne bayan da aka kasa samun jituwa kan tafiyar da gwamnati, a saboda haka nan da kwanaki 70 za a gudanar da sabon zaben 'yan majalisar domin kafa wata sabuwar gwamnatin"
Rahotanni sun ce za a gudanar da sabon zaben 'yan majalisar ne a ranar 25 ga watan Satumban wannan shekarar, bayan marabus din shugaban gwamnatin kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tanada.
Mario Draghi wanda kawancen jam'iyyun da ke mulki suka juyawa baya ya bayyana cewa "yana alfahari da aikin da ya yiwa gwamnatin kasar karkashin jagorancin shugaban kasa."