Tsananin yanayin zafi ya kai ga dalibai faduwa suna suma, lamarin da ya sanya gwamnatin Sudan ta Kudu ta dauki matakin rufe ukannin makarantun kasar. A kalla dalibai 12 ke faduwa su suma a duk rana a babban birnin kasar Juba. Wannan dai shi ne karo na biyu da kasar ta dauki wannan matakin, inda a watan Maris din 2024, aka rufe makarantun sakamakon tsananin zafin da ke iya kaiwa digiri 40 bisa ma'aunin celsius. Yawancin makarantu a Sudan ta Kudu an gidan su ne da kwanuka, kuma babu lantarkin da za a iya amfani da shi wajen kunna na'ura mai sansaya wuri.
Tuni dai minista muhalli ta kasar Josephine Napwon Cosmos ta shawarci jama'a da su takaita zirga-zirga da tsakar rana da ma yawaita shan ruwa.